Za mu janye daga MDD — Mugabe

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe, shine shugaban kungiyar tarayyar Africa AU mai barin gado.

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya ce Africa za ta janye daga Majalisar Dinkin Duniya idan har aka ci gaba da watsi da bukatun nahiyar.

Shugaban ya yi wannan jawabi ne a taron kungiyar Tarayyar Africa wanda shugabannin kasashen nahiyar ke halarta a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia.

Mista Mugabe, wanda shine shugaban Tarayyar mai barin gado, ya kara ce da cewa Africa ba za ta ci gaba da zama abin da ya kira 'mamba ta jeka-na-yi-ka ba', a majalisar ta kasa-da-kasa.

Robert Mugabe ya yi gargadi da cewa dorewar majalisar ya dogara ne ga samar da daidaito a tsakanin mambobinta.

Duk da haka, Shugaba Mugabe ya yabi babban sakataren majalisar Ban Ki Moon bisa damuwarsa ga kyautatatuwar rayuwa a Africa.