An soma yakin neman zabe a Nijar

Image caption Hoton dan takarar shugaban kasa a Nijar

A jamhuriyar Nijar, an bude yakin neman zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki a hukumance, kuma tuni bangaren masu mulki da na 'yan adawa suka dukufa a shirye-shiryensu na shiga zaben, wanda za a yi a ranar 21 ga watan Fabrairu.

'Yan takara goma sha biyar ne za su tsaya a zaben shugaban kasar, ciki har da shugaba mai ci, Alhaji Mahamadou Issoufou.

A hirar da ya yi da BBC, ministan sadarwa na kasar Malam Yahuza Sadisu Madobi, jigo a jam'iyyar RSD Gaskiya, da ke cikin kawancen masu mulki na MRN,yace gwamnati ta shirya tsaf dan tunkarrar zaben da ke tafe.

Ya kara da cewa duk wani mataki da ya kamata a dauka dan a gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali, gwamnatin shugaba Mahamaou Issoufou ta dauka.

Malam Yahuza yace tuni kuma gwamnati ta tanadarwa hukumar zaben kasar duk kayan aiki da ta ke bukata, dan tabbatar da ba a samu wata tangarda ba a lokacin zabe.

Kana kuma kura-kuran da aka gano a jikin rijistar zabe, su ma an gyara su lokaci kawai ake jira.

Ta fuskar tsaro kuwa, Malam Yahuza ya ce an tanadi matakan tsaro a dukkan sassan kasar dan gudun tada fitana.