Har yanzu yankin Ogoni na cikin matsala

Malalar mai Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Al'umar da ke zaune a wuraren da malalar mai ta lalata na cikin damuwa.

A Nigeria, masu fafutukar kare muhalli a yankin Naija Delta na kudancin kasar, suna korafi cewa ba a sanya jama'ar yankin a shiye-shiryen da ake yi na tsaftace wuraren da malalar mai ta gurbata ba, a sakamakon hakar mai da ake yi a yankin.

Ko a 'yan kwanakin nan ma, sai da Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada alwashin gwamnatinsa na yin aiki da shawarwarin da aka bayar, a karkashin shirin nan na Majalisar Dinkin Duniya kan muhalli, game da batun tsaftace yankin Ogoni da sauran sassan da malalar danyen mai ta lalata.

Masu fafutukar sun ce, an dade ana yi wa jama'ar yankin alkawarin za a shawo kan matsalar amma har yanzu gafara Sa ake yi ba su ga kaho ba.

Matsalar malalar mai dai ta lalatawa mazauna yankin Ogoni da kewayen saa gonakinsu, da ruwan da masunta ke amfani da shi dan kamun kifi.

Harwayau, babu tsaftataccen ruwan sha da suke amfani da shi, saboda matsalar ta malalar mai.

A baya ma, hukumar kare hakkin bil'adama Amnesty International ta yi kira ga kamfanin Mai na Shell, da ya tabbatar ya kwashe dagwalon mai a yankin Ogoni.