Tattaunawar Sulhu da 'yan adawar Syria

Wakilai 'yan adawa masu zaman tattaunawa a Geneva Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wakilai 'yan adawa masu zaman tattaunawa a Geneva

Manyan kungiyoyin 'yan adawar Syria sun isa Geneva don halartar taron tattaunawar sulhun da Majalisar dinkin duniya ke daukar nauyi.

Kwamitin tattaunawar na 'yan adawar ya ce zasu tattauna da hukumomin ne kawai, kana ba zasu tattauna kai tsaye da gwamnatin shugaba Assad ba.

Mai magana da yawun kwamitin koli na tattaunawa na 'yan adawar ya ce yunwa na hallaka kananan yara saboda kawanyar dakarun gwamnati da kuma hare-hare ta sama da kasar Rasha ke kaiwa.

Ya ce 'yan adawar na Geneva ne don kawo karshen abubuwan--kafin su shiga tattaunawar.

Mutane fiye da dubu dari biyu da hamsin ne suka mutu, yayin da miliyan goma sha daya suka tsere daga gidajensu a cikin kusan shekaru biyar din da aka shafe ana yaki a kasar Syria.

Yakin basasar kasar Syria shine babban ummul haba'isin matsalar kaurar jama'a zuwa kasashen Turai.

'Yan cirani akalla 39 ne da suka hada da kananan yara suka nutse a ranar Asabar cikin tekun Aegean yyainda suke kokarin ketarawa zuwa kasashen Turkiyya da kuma tsibirn Lesbos na kasar Girka.