Zika- Za ayi wasannin Olympics a Brazil

Ana gwaji kan cutar Zika Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A kasar Uganda aka fara gano cutar Zika, ta dalilin saurayen da ke yada ta a dajin Zika na kasar.

Hukumar wasannin motsa-jiki na duniya ta tabbatar wa tawagogin 'yan wasan da za su halarci gasarta a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil bana cewa babu abin da zai same su, duk da annobar Zika da ta barke a kasar.

Sai dai bangaren kula da lafiya na hukumar ya shawarci mahalarta gasar da su dauki matakan kare kansu daga sauro a lokacin da suka shiga kasar.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa cutar Zika na bazuwa a yankin kamar wutar-daji.

Wakilin BBC ya ce wannan bayanin da Hukumar wasannin motsa-jikin ta yi zai kwantar da hankalin mahukunta a Brazil, wadanda ke fama da matsalar tattalin arziki da rikicin siyasa.