Mutane 45 sun mutu a wasu hare hare a Syria

Harin kunar bakin wake a Syria Hakkin mallakar hoto AP

Wasu hare haren bama bamai da yawa sun halaka mutane akalla 45 sannan kuma ya jikkata wasu fiye da dari daya a gundumar Sayida Zeinab a bayan birnin Damascus a kusa da wuri mafi tsarki ga yan Shi'a a Syria.

Kungiyar IS ta ce ita ta kai hare haren.

Wakilin BBC a wajen ya bayyana ganin gine - ginen da ke cin wuta da kuma konannun motoci.

Ya ce an kai wa wani mazaunin soji hari.Bashar al Jaafari, shugaban tawagar gwamnati a wajen tattaunawar zaman lafiyar da ake yi a Geneva, ya ce harin ya tabbatar da alaka tsakanin yan adawa da yan ta'adda.

Hubbaren Sayida Zeinab dai na tattare da kabarin jikar Annabi Muhammad (SAW).

Haka kuma 'ya ce ga Ali, wanda yan shi'a suka yi imanin shi ne sahinin mai gadon Annabi.