Majalisar dokokin Myanmar ta fara aiki

Image caption Majalisar dokokin Myanmar

'Yan majalisar dokoki daga jam'iyar National League for Democracy - wacce Aung San Suu Kyi ke jagoranta - sun a kasar Myanmar fara aiki a zauren majalisar watanni uku bayan samun galabar da suka yi a zaben da aka gudanar mai cike da tarihi.

Ana sa ran za su fara shirye-shiryen kafa zababbiyar gwamnatin Myanmar ta farko a cikin fiye da shekara 50.

Daya daga cikin ayyukan majalisar na farko shi ne zaben shugaban kasar da zai maye gurbin Thein Sein, wanda ya sauka daga mulki a cikin karshen watan Maris.

Har yanzu sojojin kasar - wadanda suka rike kasar tsawon shekaru - na da kaso daya bisa uku na kujerun da ake da su a zauren majalisar.

Jam'iyar Aung San Suu Kyi ta samu kashi 80 bisa dari ne yawan kujerun da aka zaba a kuri'un da aka kada a zaben na watan Nuwamba.

Amma kuma rubu'in duka kujerun za su kasance na sojoji ne, da har yanzu za su cigaba da rike manyan ma'aikatu a karkashin kundin tsarin mulki.

Shugaba mai barin gado Thein Sein ya sauka daga mukaminsa ne a karshen watan Maris, amma kuma Ms Suu Kyi, wacce ta shafe shekara 15 karkashin daurin-talala, kundin tsarin mulki ya taka mata birki daga tsayawa takarar saboda yayanta maza biyu 'yan asalin kasar Birtaniya ne na Burma ba.

A cikin shekaru 20 da suka gabata ana daukar jam'iyar National League for Democray NLD ta Aung San Suu Kyi a matsayin babbar makiyiya a yankin, an rika musgunawa tare garkame shugabannnin ta a gidan kaso.