Trump da Clinton sun yi zarra

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan takarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Republican, Donald Trump

Masu neman takarar shugabancin kasa a Amurka na yunkurinsu na karshe wajen jan hankulan masu kada kuri'a a jihar Iowa, gabanin zaben share-fage na fitar da dan takara.

Donald Trump ne ke kan gaba a tsakanin masu son yin takara na jam'iyar Republican, bayan da ya samu tagomashi daga magoya bayan jam'iyar.

Babban abokin karawarsa Senator Ted Cruz yana samun goyon baya ne daga kungiyoyi masu ra'ayin mazan jiya.

Kuri'un da aka kada a zaben na jam'iyar Democratic Party sun nuna cewa Hillary Clinton ta samu galaba kan Sanata Bernie Sanders da dan kankanen rinjaye.

A yakin neman zabensa na karshe kafin kada kuri'a, Mista Trumph ya soki yarjejeniyar da aka cimma da Iran kan kera kamamashin nukiliyarta da kuma dage mata takunkumi.

Ya ce, "Dole mu rinka tunawa a ko da yaushe cewa idan har ba a kyautata maka yadda ya kamata ba, to dole ka san abin yi. Sannan idan muna jan ragamar mulkin kasarmu kuma ba a yi mana abin da ya dace kamar yadda Iran da sauran kasashe suka yi mana ba, dole ne mu damu da kasarmu".