WHO za ta yanke shawara kan Zika

Hukumar lafiya ta duniya tana tattauwnawa domin yanke shawara kan ko za a sanya cutar Zika a matsayin wacce za a nemi agajin gaggawa a kanta.

Idan aka sanya cutar a cikin jerin cututtukan da ke bukatar daukin gaggawa a duniya, hakan zai bayar da damar samun taimakon kudade daga kungiyoyin agaji da dama.

Tunda fari dai gabanin taron, mai magana da yawun hukumar WHO Christian Lindmeier, ta ce ana bukatar karin bincike kan lamarin.

"Abin da muka sani kan Zika kadan ne saboda cutar ba ta ta'azzara ba sai a wannan karon," in ji Lindmeier.

A makon jiya ne hukumar ta WHO ta yi gargadin cewa kwayar cutar ta Zika -- wacce ake dangantawa da haihuwar yara da tawaya a Brazil -- na yaduwa cikin sauri.