Biritaniya ta amince a jirkita hallitar dan-tayi

Image caption Masana kimiya sun yi maraba da matakin

Hukumomi a Biritaniya, a karon farko sun bai wa masana kimiyya izinin jirkita kwayoyin halittar dan-tayi.

Hukumar Sha'anin Daukar Ciki da kuma Kula da Dan-tayi ta ba da izinin yin amfani da hikimar jirkita kwayoyin halitta, a wani aikin da zai duba farkon rayuwar dan-tayin.

Masana kimiyya a cibiyar bincike na fatan hakan zai zama sanadin magance matsalar rashin haihuwa.

Sai dai ba za a iya dasa dan tayin da za a yi amfani da shi din ba a cikin wata mahaifiya.