Takaitaccen tarihin Hama Amadou

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Har yanzu Amadou na kulle a gidan kaso

An haifi Hama Amadou a 1950 a garin Youri na jihar Kollo da ke jihar Tillabery.

Ya yi karatun aikin kwastam da na gwamnati a makarantar koyon aikin gwamnati, ENAM da ke birnin Yamai da kuma Babbar Cibiyar koyon aikin gwamnati ta kasa da kasa da ke birnin Paris na Faransa.

Hama Amadou ya rike manyan mukamai daban-daban na gwamnati daga 1972 har zuwa 1988, lokacin da ya zama ministan yada labarai.

A lokacin babban taron kasa na Conference National a shekarar 1991, Hama Amadou ya tsaya kai da fata wajen kare jam'iyyar MNSD-Nasara, wadda ya wakilta a wajen taron, abin da ya ba shi damar zama Babban Sakataren jam'iyyar a 1991.

Hama Amadou ya rike mukamin Firayi ministan Nijar har sau uku tsakanin 1995 da 2007, lokacin da majalisar dokokin kasar ta kada kuriar yanke ma shi kauna.

A shekarar 2008 hukumomi sun kulle shi a gidan kurkukun Koutoukale inda ya shafe watanni 10 bisa zargin cin hanci.

Daga bisani ya fice daga jam'iyyar MNSD-Nasara domin kafa jam'iyyarsa ta MODEN-Lumana .Sau uku kuma ana zabar shi a matsayin dan majalisar dokoki.

A zaben shugaban kasa na 2011 ya zo na uku, kuma ya marawa Mamahadou Issoufou baya a zagaye na biyu. Hakan ya sa ya samu mukamin shugaban majalisar dokoki har zuwa 2014, lokacin da ya fice daga kasar saboda zargin da ya ke fuskanta na kasancewa da hannu a wata badakala ta sayo jarirai daga Najeriya.

An kama shi yayinda ya koma gida a watan Nuwamban 2015,(kuma har yanzu yana tsare a gidan kason Fillingue).

A watan Satumba na 2015 ne, jam'iyyarsa ta MODEN-Lumana ta tsaida shi a matsayin dan takararta a zaben da zaa yi a ranar 21 ga watan Fabrairu 2016.