'Jonathan ya sayo jabun makamai'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana zargin mukarraban Jonathan da karkatar da kudin sayo makamai

Gwamnatin Najeriya ta yi zargin cewa tsohuwar gwamnatin da ta shude ta Goodluck Jonathan ta sayo jabun makamai ne domin yaki da Boko Haram.

A cikin wata sanarwa, ministan yada labaran kasar, Alhaji Lai Mohammed ya ce abin takaici ne a ambato Mr Jonathan na cewar an samu nasarori ne a yaki da Boko Haram saboda makaman da gwamnatinsa ta sayo.

"Makamai da kayan yakin da tsohon shugaban kasa ya ce ya sayo, galibi jabu ne ko kuma wadanda aka yi wa kwaskwarima," in ji Lai Mohammed.

Mohammed ya ce gwamnatin Buhari na da alhakin fadin gaskiya kan wannan lamarin saboda ya shafi al'umma da kuma tsaron kasa.

A cewar ministan yaki da Boko Haram bai samu nasara ba sai da gwamnatin Buhari ta hau karagar mulki.

An ambato Mr Jonathan na ikirarin cewa shi ne ya sayo makaman da gwamnatin Buhari ke amfani da su wajen murkushe 'yan Boko Haram.

Rikicin Boko Haram a cikin shekaru shida a Najeriya, ya janyo mutuwar mutane fiye da 18,000 sannan wasu fiye da miliyan uku suka rasa muhallansu.