Bam ya kashe mutane 10 a Kabul

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan Taliban na yawan kai hare-hare a Afghanistan

An kai harin bam na kunar bakin wake a Kabul, babban birnin Afghanistan.

An kai hari ne hedikwatar hukumar 'yan sanda masu wanzar da zaman lafiya, watau hukumar da ke kokarin magance hare-haren kungiyar Taliban.

Mataimakin ministan harkokin cikin gida Ayoub Salangi, ya ce an kashe mutane goma kuma mutane ashirin sun jikkata.

"A nan wajen bam ya fashe, da idona dai na ga gawarwaki uku a kasa, sannan kuma na ga mutane da dama da suka ji rauni," in ji shaida.

A watan da ya gabata ne aka kai jerin hare-hare a birnin na Kabul.