Takaitaccen tarihin Mahamadou Issoufou

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Issoufou na neman tazarce a karo na biyu

An haifi Mahamadou Issoufou a 1951 a garin Dan Daji na jihar Illela da ke yankin Tahoua a jamhuriyar Nijar.

Ya karanta fannin ilimin hako ma'adanai a birnin Saint Etienne na Faransa inda ya samu digirin Injiniya a 1979.

Bayan ya koma gida, Mahamadou Issoufou ya rike manyan mukamai daban-daban da suka hada da Direktan sashen ma'adanai a Ma'aikatar ma'adanai da masana'antu daga 1980 zuwa 1985 da kuma Babban Sakataren kamfanin hako Uranium na Somair da ke Arlit daga 1985 har ya rike mukamin Direkta a 1991 zuwa 1992.

Tun da Nijar ta koma kan tafarkin Demokradiyya a 1993, Mahamadou Issoufou ya tsaya takarar shugabancin kasa a kowanne zaben da aka yi.

Ya jagoranci jam'iyyar PNDS-Tarayya tun daga lokacin da aka kafa ta a shekarar 1990 har zuwa lokacin da ya hau kan karagar mulki a 2011.

Kafin ya zama shugaban kasa, Mahamadou Issoufou ya rike manyan mukaman siyasa da suka hada da Firayim minista daga 1994 zuwa 1995 da shugaban majalisar dokoki daga 1995 zuwa 1996.

Daga 1999 har zuwa 2010, ya kasance dan majalisar dokokin kasar, kuma shi ne madugun 'yan adawa.

A watan Nuwamba na 2015 ne, jam'iyyar PNDS-Tarayya ta tsaida shugaba Mahamadou Issoufou a matsayin dan takararta na zaben a ranar 21 ga watan Fabrairu na 2016. Yana da mata 2 da 'ya'ya 4.