Takaitaccen tarihin Mahamane Ousmane

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ousmane na son ya kara shiga fadar shugaban Nijar

An haifi Mahamane Ousmane a shekarar 1950 a Zinder. Ya karanta ilimin lissafi da fasali a Faransa da kuma Canada.

Shi ne shugaban kasar Nijar na farko da aka zaba bisa tafarkin Demokradiyya. Ya shafe kasa da shekaru uku ne kacal a kan karagar mulki daga 1993 zuwa 1996, lokacin da sojoji suka yi ma shi juyin mulki.

Kafin ya zama shugaban kasa, Mahamane Ousmane ya rike mukamai daban-daban a fadar Firayi minista da kuma ma'aikatar fasali.

An zabe shi shugaban jam'iyyar CDS-Rahama a watan Fabrairun 1991.

Ya yi takarar shugaban kasa a karkashin inuwar ta jam'iyyar CDS-Rahama a dukannin zabubukan da aka yi, tun bayan da aka hambarar da shi daga mulki, kuma ya rike mukamin shugaban majalisar dokoki daga 1999 zuwa 2009.

Jam'iyyar CDS-Rahama, ta fuskanci baraka, sakamakon rikicin shugabancin jam'iyyar tsakanin Mahamane Ousmane da matimakinsa, Abdou Labo, abun da ya kai batun gaban shari'a.

Bayan kotu ta ba bangaren Abdou Labo gaskiya, bangaren Mahamane Ousmane ya daukaka kara, kuma har yanzu maganar tana gaban sharia.

A watan Disamba na shekarar 2015 ne jam'iyyar MNRD- Hakuri ta tsaida Mahamane Ousmane a matsayin dan takararta na zaben da ke tafe. Jaririyar jam'iyya ce da aka kafa shekaru 3 da suka wuce.

Mahamane Ousmane yana da mata guda da 'ya'ya 11.