Kasafi: Nigeria na tattaunawa da Bankin Duniya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Faduwar farashin mai ka iya tasiri a kasafin kudin Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta ce ta fara tattaunawa da Bankin Duniya a kan yiwuwar karbar bashi domin cike gibin kasafin kudin kasar na shekarar 2016.

Wata sanarwa da kakakin ministar kudin kasar, Festus Akanbi ya fitar, ta ce sabanin rahotannin da ake bazawa, gwamnati ba ta gabatar da bukatar neman bashi ba ga Bankin Duniya, amma kuma akwai yiwuwar karbar bashin domin gudanar da ayyukan raya kasa wadanda za su habaka tattalin arzikin Najeriya.

Sanarwar ta ce Bankin Duniyar na daya daga cikin zabin da Nijeriya ta ke da shi a matsayinta na wakiliya.

Faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya dai ya sanya tattalin arzikin kasar ya fada mawuyacin hali.

Sabuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi niyyar cike gibin kasafin kudin domin daidaita tattalin arzikin kasar, amma gibin da ake samu tsakanin kudaden shigarta da kudaden da gwamnatin za ta kashe na kara girma.

Shugaban kasar dai ya zargi jami'an tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan da almundahana da kudaden kasar, lamarin da ya jefa ta cikin halin kaka-na-ka-yi, ko da ya ke tsohuwar gwamnatin ta sha musanta zargin.