An soma tattaunawa kan makomar Syria

Hakkin mallakar hoto
Image caption Babu tabbas ko za a cimma sakamako mai dadin ji a kan Syria

Jakadan Majalisar dinkin duniya na musamman na tattaunawa a Geneva tare da kungiyar 'yan adawar Syria bangaren da Saudiyya ke goyon baya.

Jakadan majalisar Staffan de Mistura, na kokarin ganin ya kaddamar da wani shirin sasantawa tsakanin gwamnatin Syria da wadancan 'yan adawar amma ta hanyar masu shiga tsakani.

Gabannin fara ganawar wata mai fafutuka a bangaren 'yan adawa Farah Atassi, ta shaida wa manema labarai cewa kungiyoyin adawa za su sake rokon jakadan majalisar dinkin duniya don yin kokarin ganin an kawo karshen rikicin.

Kwamitin shiga tsakani da Saudiyya ke goyon baya na shirin gabatarwa da Mista De Mistura wasu tsare-tsare don inganta halin da al'umma ke ciki a Syria, kafin fara waccar tattaunawar.

Kwamitin ya kuma bukaci gwamnati ta dage takunkumin da ta sanya a garuruwan da ke karshin ikon 'yan tawaye domin a samu damar kai kayan agaji da kawo karshen hare-haren sama ta kuma saki fursunoni.