Mutumin da ya fi kowa iya girki ya mutu

Image caption A watan Disamba ne gidan sayar da abincin Mista Violier ya lashe kyautar wanda ya fi iya dafa abinci.

Mista Benoit Violier, mutumin da gidan sayar da abincinsa ya lashe kyautar wanda ya fi iya yin girki a duniya, ya mutu.

An gano gawar Mista Violier ne a gidansa.

Mista Violier, mai shekara 44, shi ne mai gidan sayar da abinci na Restaurant de l'Hotel de Ville da ke Crissier, kusa da birnin Lausanne na kasar Switzerland.

A watan Disamba ne aka zabi gidan sayar da abincinsa a matsayin wanda ya fi iya dafa abinci a duniya.

'Yan sandan Switzerland sun ce mai yiwuwa Mista Violier, wanda aka haifa a kasar Faransa, ya harbe kansa ne.

Ya mutu me wata shida bayan mutuwar babban uban gidansa, Philippe Rochat, wanda kuma shi ne shugaban gidan sayar da abincin na Restaurant de l'Hotel de Ville kafin Mista Violier.