An ayyana dokar ta baci a kan cutar Zika

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Darakta janar ta hukumar lafiya ta duniya Margaret Chan

Hukumar lafiya ta duniya ta ayyana dokar ta baci ta duniya kan yaduwar cutar zika da irin illar da take yi wa jarirai.

Hukumar ta ce ana bukatar hada karfi da karfe tsakanin kasashen duniya domin magance yaduwar cutar.

Margaret Chan ita ce Darakta janar ta hukumar WHO tace "A matakin magance wannan cuta dole ana bukatar kara lura da gano hanyoyin kamuwa da cutar da illolin da take jawowa da kuma kara kaimi wajen magance yawaitar sauro, da kuma kokarin ganin an gano hanyoyin gwaji da na riga-kafi domin kare mutane daga illarta musamman masu juna biyu."

A makon jiya ne hukumar ta WHO ta yi gargadin cewa kwayar cutar ta Zika -- wacce ake dangantawa da haihuwar yara da tawaya a Brazil na yaduwa cikin sauri.

A wani labarin kuma gwamnatin Brazil ta ce babu wata barazanar cewa za a soke gasar wasan Olympics saboda cutar Zika.

Amma kuma babban jami'in fadar shugaba Dilma Rousseff, (Jaques Wagner) ya shawarci mata masu juna biyu da kada zu yi bulaguro zuwa kallon wasannin, wanda za a gudanar a wani yanayin hunturu da akasari ba samun yaduwar sauraye ba.

A baya dai shugaba Rousseff ta umarci jami'an duba gari da su yi amfani da karfi wajen kutsawa cikin kwangwaye don duba inda saurayen ke kyankyasa.

Ma'aikatar lafiya ta kasar Brazil ta ce da duba yiwuwar hayaiyafar sauro a kusan kashi 25 bisa dari na gidaje miliyan 49.