Mutumin da ya kai Apple kara ya samu nasara

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Agogon da kamfanin Apple ke kerawa

Mutumin da ya kai kamfanin Apple kara a kan tsagewar da sabon agogonsa mai komai da ruwansa ya yi, ya samu nasara a shari'ar.

Gareth Cross ya gano tsagewa a agogon na sa ne bayan kwanaki goma da siyansa a kan kudi fan dari uku da talatin da tara.

Da farko kamfanin na Apple ya mayarwa mutumin martani inda ya ce matsalarda ta samu agogon bata daga cikin yarjejeniyar kayayyakin da yake sayarwa.

Daga nan ne sai Mr Cross ya yi nasarar gabatar da korafinsa a gaban wata kotu da ke sauraron kararrakin da suka shafi cinikin kananan kayayyaki.

Yanzu haka dai kamfanin na Apple zai Mr Cross fan dari hudu da ashirin da tara, wato kudin agogon da kuma kudin shigar da kara.

Kuma zai biya wadannan kudade ne zuwa nan da 22 ga watan Fabrairun da muke ciki.

Mr Cross ya ce an shafe watanni shida ana shar'ar, ya kuma bayyanawa BBC cewa bai ga dalilin da ya sa kamfanin ya kai shi kara ba, dan haka ne ya tsaya kai da fata na ganin ya kwato 'yancinsa.