Garan-bawul kan dokar luwadi a India

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gamgamin 'yan luwadi a Indiya

Kotun kolin Indiya ta amince ta sake duba wata doka tun ta zamanin mulkin mallaka da ta amince da a daure duk wanda aka kama yana luwadi har tsawon shekara 10 a gidan yari.

Wani kwamitin alkalai biyar ne za su yi duba kan lamarin.

A shekarar 2009 ne kotun kolin da ke birnin Delhi ta kawo karshen dokar wadda aka dauki tsawon shekara dari da hamsin da biyar ana aiwatar da ita, tana mai cewa ta take hakkokin bi'adama.

Amma a shekarar 2013, kotun kolin ta sake janye hukuncin, inda ta ce majalisar dokoki ke da alhakin sauya dokar ba kotuna ba.

Duk da cewa ba a cika amfani da hukuncin dokar ba, amma 'yan luwadi na cewa ana amfani da ita wajen muzguna musu.