Isra'ila na tura 'yan gudun hijrar Afrika zuwa wasu kasashe

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan gudun hijrar Afrika

Sashen BBC na Afrika ya samu shaidu da suka nuna cewa kasar Israila na turo wasu 'yan Afrika dake cirani wadanda ba'a maraba da su zuwa wata kasa ta dabam a wani shiri da ake yi a asirce, wanda kuma mai yiwu wa ya saba wa dokokin kasa da kasa.

A yanzu haka akwai kimanin 'yan cirani dubu 45 'yan kasar Eritrea da Sudan da ke kasar Israila.

Gwamnatin Israilan dai ta ki ta bayyana ko wace kasa ce aka shirya wannan tsarin da ita, sai dai BBC ta tattauna da wasu mutane wadanda suka ce an tura su zuwa Rwanda da kuma Uganda.

Can a cikin hamadar Negev da ke Isra'ila, akwai wani kurkuku na kare kukanka wanda ke tsakiyar hamadar kuma yana da tazara daga babban birnin kasar wato Tel Aviv.

Anan wajen akwai 'yan gudun hijra daga kasshen Afrika da ake tsare da su wadanda yawan su ya kai kusan dubu uku.

Katafaren gini ne da aka kewaye da waya mai tsini,Sannan wurin na tsakiyar wani sansanin sojoji.

Wadanda ke wajen ba a barinsu yin aikin komai, 'yan abubuwan da suke kalilan ne.

Dukkaninsu maza ne, kuma yawancinsu shekarunsu bai wuce ashirin da doriya ba zuwa talatin da daya ko biyu haka.

Suna kuma magana ne da harshen Hebrew a tsakaninsu.

Akwai wasu da damansu dake zaune suna sauraron kade-kade, wasu kuma na girki yayinda wasu kuma na karta.

Ba'a barin 'yan jarida shiga cikin kurkukun

Mutane da dama dai na cewa sun je Isra'ila ne domin neman mafaka daga rikiicn da ake yi a kasarsu.

Amma kuma gwamnatin kasar bata bayar da mafakar da ta ce domin kaso daya cikin na 'yan gudun hijrar ta ke bawa mafaka.

Gwamnatin kan ce karin yawaitar 'yan gudun hijrar da suka fito daga kasashen Eritiriya da Sudan zuwa kasarsu na haifar da barazana ga harkokin tsaronsu.

Ana dai tsare 'yan gudun hijra a wannan waje mai kama da kurkukun kare kukanka tsawon shekara guda.

Daga nan kuma sai a barsu ko su koma gida ko kuma su tafi wata kasar daga cikin kasashen Afrika su zauna a can. Idan har suka amince da wannan zabi to gwamnatin Isra'ilan to sai a basu dala dubu uku da dari biyar.

Idan kuwa suka ki barin kasar to sai a tura su zaman gidan kaso na din-din-din.