'Jordan za ta daina karbar 'yan gudun hijira'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kimanin kashi 20 cikin dari na mutanen Jordan 'yan gudun hijira ne

Sarki Abdullah na Jordan ya shaida wa BBC cewa kasarsa ta kai kololuwar kokarinta wajen yawan 'yan gudun hijirar Syria da za ta iya karba.

A cewar Sarkin na Jordan, saboda haka kasarsa ba za ta sake karbar wasu 'yan gudun hijirar ba, muddin ba ta samu wani taimako ba.

Taimakon da ya ce ya kamata ya hada da samar da ayyukan yi ga 'yan kasarsa.

Sarkin yana wannan kira ne gabannin wani taro na kungiyoyin agaji na kasa da kasa da za a yi a London a ranar Alhamis.

Kasar ta Jordan da ke makotaka da Syria ta karbi dubban 'yan gudun hijirar da yaki ya raba da muhallansu.