Kotu ta ci gaba da sauraron karar Farouk Lawan

Image caption Farouk Lawan bai kara komawa majalisa ba

Wata babbar kotu a Najeriya ta soma sauraron tuhumar da ake yi wa tsohon dan majalisar wakilai, Farouk Lawan, bisa zargin da ake yi masa na karbar cin hancin a wurin Mista Femi Odetola.

Ana zargin Lawan ne da karbar dala dubu 620 daga hannun shahararren dan kasuwar, a lokacin da shi Farouk Lawan din yake shugabantar kwamitin binciken badakalar kudaden tallafin mai a shekarar 2012.

Sai dai kotun ta dage zamanta zuwa ranar tara ga watan da ake ciki, bayan lauyoyin wanda ake zargi sun kalubalanci wasu takardu da masu gabatar da kara suka gabatarwa kotun a matsayin shaida.

Baya ga Lawan akwai akawun kwamitin da shi ma ake zarginsa a shari'ar da ake tuhumarsu.

Tun a watan Fabrairun 2013 ake gurfanar da mutanen biyu gaban kuliya a zargin da ake musu na kokarin karbar cin hanci daga Mista Otedola, domin a cire sunan kamfaninsa daga cikin jerin sunayen kamfanonin da ake zargi a badakalar kudaden tallafin mai a Najeriya.