An yi garkuwa da jirgin ruwa a Calabar

Image caption Masu fafutuka a yankin Niger Delta

Rahotanni daga kudancin Najeriya na cewa wasu 'yan bindiga sun sace wani jirgin daukar kaya kuma suka yi garkuwa da ma'aikatan jirgin 'yan kasar waje da ba a san adadinsu ba.

'Yan bindigar na barazanar tarwatse jirgin tare da halaka ma'aikatan muddin hukumomin kasar basu sako jagoran 'yan awaren kasar Biafra ba.

Tun a ranar Juma'a ne dai aka sace jirgin a yankin ruwan Calabar.

Kuma kafin a yi wa 'yan fafutukar kwato 'yancin Niger Delta afuwa shekaru biyar da suka wuce, sace jirage tare da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa ya zama ruwan dare.