'Ba a nuna fifiko kan 'yan takarar Nijar'

Image caption A ranar 21 ga watan Fabrairun da muke ciki ne za a yi zaben shugaban kasa a Nijar

Hukumar sadarwa ta Nijar CSC, ta ce ta dauki matakan da 'yan takaran shugaban kasa za su tallata kansu a kafofin yada labarai ba tare da nuna fifiko ba.

Shugaban hukumar Malam Abdurahman Usman, ya ce kowane dan takara a zaben shugaban kasar zai iya tallata kansa a kafofin yada labarai mallakar Gwamnati na wasu lokuta kuma ba tare da biyan kudi ba.

Malam Abdurahman ya kuma kara da cewa hukumar na tattauna wa da kafafen yada labarai masu zaman kansu, domin cimma yarjejeniya wajen ganin sun yi adalci ga 'yan takara wajen kudaden da za su biya.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara yakin nemen zabe a kasar.

'Yan takara goma sha biyar ne ke fafatawa a zaben na wannan shekara.