Malamai sun koka kan cire sassan jikin mutane

Hakkin mallakar hoto BBC Nurah Ringim
Image caption Yaron da aka cirewa idanu a Zaria

Malaman Addinin Musulinci da na Kirista a Najeriya, na ci gaba da nuna damuwa kan yadda wasu mutane da ake zargi matsafa ne ke cire sassan jikin mutane domin yin tsafi.

Malaman sun nuna damuwar ne bayan rahotanni sun nuna yadda ake ci gaba da cire sassan jikin mutane, inda ko da a baya bayan nan sai da aka kwakule idanun wani karamin yaro a garin Zariya na jihar Kaduna.

Wasu Malamai da BBC ta yi hira da su sun bayyana cire sassan jikin mutane domin yin tsafi da su a matsayin babban laifi.

Shekh Dahiru Usman Bauchi, wani fitaccen Malamin addinin Islama, ya ce, "Wanda ya hada tsafi da gabobin mutane, to ya yi laifi guda biyu: ya yi shirka sannan ya cuci mutanen da ya cire sassansu. Idan aka cire hannu ko kafa ko wani sashe na jikin mutum bayan ya mutu, daidai yake da idan aka cire su idan mutum yana da rai saboda dan adam yana da alfarma."

Shi ma Malamin addinin Kirista, Rabaren Shu'aibu Bel, ya ce duk mutumin da ya cire sassan jikin mutane domin yin tsafi da su, ba zai gama da duniya lafiya ba.

Ya kara da cewa, "Abin da duk mutum ya shuka shi zai girba. A ranar lahira za a yi masa mummunar shari'a, kuma a duniya ma Allah yana iya hukunta duk wani laifi; ana iya gajarta kwamnakinmu, wani lokacin abubuwa munana suna iya faruwa a kanmu".

Rabaren Shu'aibu Bel ya ce kasashen duniya suna kallon 'yan Najeriya a matsayin masu bin addini sau-da-kafa, sai dai halayen 'yan kasar na cin karo da addininsu.