'Yan adawar Syria sun zargi Rasha da kai hare-hare a kasarsu

Hakkin mallakar hoto
Image caption Tattaunawar sulhu a kan Syria

Wakilai daga kungiyoyin 'yan adawar Syria sun ce sun yi ganawa mai ma'ana da manzon musamman na MDD, Staffan de Mistura.

Suna kuma jiran sakamakon tattaunawar Majalisar Dinkin Duniyar da hukumomin kasar a ranar Laraba kafin su yanke shawarar ko za su shiga zaman tattaunawar sulhu da za a yi nan gaba a Geneva.

Yayinda yake jaddada rashin jituwa tsakanin bangarorin biyu, mai magana da yawun 'yan adawar Salim al-Muslat, ya zargi kasar Rasha da kasancewa wani sabon Hitler a Moscow, tare da taimakawa wani Hitler'n a kasar Syria

Salim al-Muslat ya cigaba da cewa '' Mun zo nan don tattaunawa da manzon musamman na MDD, kan batun dakatar da kai hare-hare ta saman da Rasha ke kaiwa kasar Syria".