Kada a bari tattaunawar sulhu kan Syria ta rushe

Taron sulhu  kan kasar Syria a zauren Majalisar Dinkin Duniya Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Taron sulhu kan kasar Syria a zauren Majalisar Dinkin Duniya

Jakadan musamman na Majalisar Dinkin Duniya Staffan de Mistura, yayi kira da a dau matakan ganin tattaunawar sulhu kan Syria bata rushe ba.

A wata hira da gidan talabijin na Swiss, Mr de Mistura ya ce muddin a wannan karon suka gaza, toh babu wani sauran fata game da zaman lafiyar kasar Syria.

Yana magana ne bayan da wakilan 'yan adawa suka soke batun tattaunawar da Majalisar Dinkin Duniya a rana ta biyu ta zaman tattaunawar Geneva.

A baya dai wakilan gwamnatin kasar Syria sun ce har yanzu suna jiran ajandar taron, da kuma cikaken jerin sunayen mahalarta taron.

A kasar ta Syria, dakarun gwamnati na kara dannawa cikin birnin Aleppo inda yan tawaye ke rike da iko.