Rikicin Libya na yi mana barazana—Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi gargadin cewa rikicin da ake fama da shi a Libya yana zamowa wata babbar barazana ga Afrika da Turai.

Da yake jawabi a gaban majalisar dokokin tarayyar Turai a Strasbourg, shugaba Buhari ya yi magana a kan yadda ake baje kolin makamai a kudancin Libya, al'amarin da ke shafar dukkan yankin da ya hada har da Najeriya, wadda ita ma ke yaki da kungiyar Boko Haram.

Ya yi kira da a kara daukar matakai don kawo mafita ta warware rikicin Libya, inda bangarori biyu da ke adawa da juna suke fada a kan mulki, yayin da kungiyar IS kuma take amfani da damar wajen mamaye kasar.

Shugaba Buhari kuma ya tabbatarwa da kungiyar tarayyar turai cewa gwamnatinsa na iya bakin kokarinta wajen kare hakkin bil adama a yakin da ta ke yi da Boko Haram.

Ga rahoton Suwaiba Ahmed
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti