Ban yi wa 'yan Nigeria alkawari 222 ba —Buhari

Hakkin mallakar hoto Screen Grab
Image caption Shugaba Buhari ya sha alwashin yaki da 'yan Boko Haram.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya musanta ikirarin da wata cibiya ta yi cewa ya yi alkawari 222 a lokacin da yake yin yakin neman zabe.

Cibiyar mai suna Cibiyar Dimokradiyya da Ci gaban Al'uma, a karkashin wani shiri na hadin gwiwa da wasu kungiyoyi masu zaman kansu wanda ake kira BuhariMeter, ta fitar da wani rahoto kan abin da ta ce alkawura 222 ne da shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa al'ummar Najeriya, tana mai cewa a cikinsu, alkawari daya kawai ya aiwatar zuwa yanzu.

Sai dai mai magana da yawun shugaban kasar, Malam Garba Shehu, ya shaida wa BBC cewa Shugaba Buhari ya dauki manyan alkawura uku ne kawai, kuma yana kokarin ganin ya cika su.

Malam Garba Shehu ya ce, "Wanda duk ya ji maganar da suke yi ya san sharholiya kawai suke yi. A lokacin da Shugaba Buhari zai cika kwana 100 a kan mulki sun buga wata kasida cewa wai ya yi alkawura 100 da zai cika a cikin kwana dari, kuma mun fito muka ce karya suke yi. Saboda kafin zabe Shugaba Buhari ya je London inda aka tambaye shi ko ya yi wannan alkawari ya ce shi abin da yake so shi ne a ba shi mulki, kuma zai yi kokarin inganta rayuwar 'yan Najeriya."

Ya kara da cewa manyan alkawura uku da Shugaba Buhari ya yi su ne samar da tsaro da yaki da cin hanci da rashawa da inganta tattalin arziki.

Ku saurari cikakkiyar hirar da Haruna Tangaza ya yi da Malam Garba Shehu:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti