Boko Haram: An rufe makarantu 136 a Kamaru

Hakkin mallakar hoto Nig Govt
Image caption A bara shugaba Buhari ya kai ziyara a Kamaru saboda yaki da Boko Haram

Hukumomi a Jamhuriyar Kamaru sun ce an rufe makarantu akalla 136 a cikin kasar saboda hare-haren 'yan Boko Haram.

Makarantun da aka rufe sun hada da na firamare da na sakandare.

Galibin makarantun suna yankuna takwas ne a lardin arewa mai nisa inda 'yan Boko Haram ke tafka ta'asa.

Yawancin makarantun - kamar wadanda ke kauyen Kerawa - ana amfani da su ne a matsayin sansanonin 'yan gudun hijirar Najeriya wadanda suka tsallaka cikin Kamaru.

Hukumomi a Jamhuriyar Kamaru sun ce 'yan kungiyar Boko Haram sun kashe kimanin mutane 1,200 a kasar tun daga shekarar 2013.