Masana'antu sun koka da karin kudin wuta

Hakkin mallakar hoto
Image caption Masana'antar yin tufafi a Nigeria

wasu daga cikin kamfanonin da ke rarraba wutar lantarkin sun ce sune suka bukaci a kara kudin wuta, domin su samun kudaden da zasu yi amfani da su, don inganta hanyoyin wutar lantarki a kasar.A Nigeria, kungiyar ma su masana'antu ta kasar ta soki matakin karin kudin wutar lantarki da hukumar da ke sa ido kan samar da wutar lantarki a Najeriyar ta yi.

A farkon wannan watan ne dai hukumar da ke sa ido kan samar da wutar lantarki ta sanar da kara kudin wutar lantarkin da kusan kashi 45 cikin 100.

Sai dai kungiyar masu masana'antu ta ce matakin zai shafi masana'antun kasar wadanda ke neman farfadowa, bayan shafe shekaru suna cikin mawuyacin hali.

Alhaji Ali Sufyanu Madugu, mataimakin shugaban kungiyar masu masana'antun ta kasa a Najeriya, ya shaidawa BBC cewa ba su amince da wannan karin ba, kuma yanzu haka ya ce maganar karin kudin wutar na gaban Kotu.

Sai dai wasu daga cikin kamfanonin da ke rarraba wutar lantarkin sun ce sune suka bukaci a kara kudin wutar domin su sami kudaden da za su yi amfani da su, don inganta hanyoyin wutar lantarki a kasar.