An soma gina babbar katanga a Bagadaza

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan IS na yawan kaddamar da hare-hare a Bagadaza

Gwamnatin Iraki ta fara gina wata katangar tsaro wadda ta ce a karshe za ta zagaye dukkan babban birnin kasar, Bagadaza.

Wani rahoto ya ce aikin zai hada da tona rami mai zurfin mita biyu a gaban katangar.

Makasudin yin hakan shi ne ta yadda 'yan kungiyar IS ba za su sami sauki wajen shiga birnin ba balle har su sami damar kai hare-hare.

Katangar za ta zama wani shamaki na hana shiga da kuma saukaka binciken ababen hawa.

Wakilin BBC ya ce: "Kungiyar IS na yawan kai hare-hare birnin Baghdad, kuma a wani hari da suka kai a watan da ya gabata ne suka kashe a kalla mutane 18 a wani rukunin shaguna."