'Kwamandojin mayakan IS sun shiga Libya'

Hakkin mallakar hoto Reuters

Wani jami'in Leken asirin Libya ya fadawa BBC cewa a 'yan watannin nan kwamandoji daga mayakan Kungiyar IS sun shiga cikin kasar daga kasashen Syria da Iraqi

Isma'il Shukri-- wanda shine shugaban hukumar leken asiri ta garin Misrata-- ya ce wasu mayakan kungiyar ta IS sun shigo har ila yau.

Ya ce shigowar ta su, ta biyo bayan matsin lambar da kungiyar ke fuskanta a yankin gabas ta tsakiya, inda kasashen duniya ke yi musu luguden wuta ta sama da kuma ta kasa

Mr Shukri ya ce mayakan IS na daukar Libya a matsayin inda za su tsira da rayukansu

Libya dai ta shiga cikin rudani ne tun lokacin da aka hanbarar da Kanar Gaddafi a shekarar 2011