Majalisar dinkin duniya ta goyi bayan Assange

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Majalisar dinkin duniya ta ce bai kamata a ci gaba da tsare Mista Assange ba.

BBC ta fahimci cewa kwamitin majalisar dinkin duniya da ke yin nazari kan zargin tsare mai shafin Wikileaks da ke kwarmata bayanan sirrin nan, Julian Assange, ya goyi bayan mutumin.

A shekarar 2012 ne Mista Assange ya nemi mafaka a ofishin jakadancin Ecuador da ke birnin London domin kauce wa fitar da shi zuwa Sweden inda ake tuhumarsa da laifin yin lalata.

Sai dai a shekarar 2014 Mista Assange ya yi korafi ga kwamitin majalisar dinkin duniya cewa "ana tsare da shi ba bisa ka'ida ba", domin kuwa za a iya kama shi da zarar ya fice daga ofishin jakadancin.

An bayar da sammacin kama shi a Biritaniya, kuma mahukuntan kasar sun ce za a kama shi din idan har ya fito daga ofishin jakadancin.

A ranar Juma'a ne ake sa ran kwamitin zai fitar da rahotonsa kan tsarewar da ake ci gaba da yi wa Mista Assange ba bisa ka'ida ba.

Kwamitin ya ce bai kamata a ci gaba da tsare shi ba.

Sai dai ofishin harkokin waje na Biritaniya ya ce yana da damar mika Mista Assange ga kasar ta Sweden da zarar ya fito daga harabar ofishin jakadancin Ecuador.