Masu gidajen burodi na yajin aiki a Kano

Kungiyar masu gidajen burodi ta jihar Kano a Najeriya ta shiga wani yajin aikin gargadi na kwanaki uku.

Ta shiga yajin aikin ne domin nuna damuwa game da abin da ta ce tashin farashin kayayyakin da ake hada burodin da su.

Yajin aikin dai ya haifar da karancin burodin a jihar, wanda kuma ya tilastawa masu sayar da shayi dakatar da sana'ar ta su a lokacin da ake yajin aikin.

Ga hotunan da Yusuf Ibrahim Yakasai