Microsoft ya sa a dawo da wayoyin Kwamfuta

Waya samfurin Ipad Hakkin mallakar hoto other
Image caption Tun a bara kamfanin ya fara samun korafi kan wayoyin na sa.

Kamfanin Microsoft ya sa a dawo da wayoyin Kwamfuta da aka saida hade da wayoyi masu kama da Ipad, bayan samun rahotanni Hamsin kan cewa wayoyin na yin tsananin zafi da kuma hayaki.

Harwayau kamfanin ya samu rahotanni Biyar da ke nuna cewa wayar da ke daukar zafi ta ke jan su.

Reshen sashen da ke kula da wayoyi na kamfanin Microsoft a Amurka, ya bukaci dukkan abokan huldar sa da su dakata da amfani da wayoyin har sai sun tuntubi kamfanin.

A karshen watan Jiya ne kamfanin ya fitar da wannan sanarwa, sai dai bai bayyana yawan korafin da ya sa mu ba game da matsalar.

Wayoyin da suke da wannan matsala dai an saida su ne tsakanin watan Mayun shekarar da ta gabata a Amurka, da kuma watan Yulin bara a kasar Canada.