Hukumar zaben Niger ta fara rabon katin zabe

A jamhuriyar Nijar hukumar zabe ta fara rarraba katunan zabe ga masu kada kuri'a a fadin kasar.

Shugaban hukumar Ibrahim Bube ne ya shaida wa BBC hakan, inda ya kara da cewa hukumar ta dauki matakan ganin an rarraba katunan ba tare da wata matsala ba.

Haka kuma nan ba da jimawa ba ne hukumar za ta fara raba kayayyakin zabe a jahohi da kuma sauran sassan kasar:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shugaban hukumar ya kuma bayyana cewa an dauki matakan da suka kamata wajen ganin kayayyakin zabe sun isa jihar Diffa da ke fuskantar barazanar Boko Haram.

Inda ya ce an dauki dukkan matakan da suka dace, domin ganin an yi zabukan lami lafiya a fadin kasar.

A ranar 21 ga watan Fabrairun da muke ciki ne 'yan kasar za su kada kuri'a domin zaben shugaban kasa da 'yan majalisar dokoki.