Nigeria ta nemi bashin dala biliyan daya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya ya shafi tattalin arzikin Najeriya

Bankin raya kasashen Afrika ya tabbatar da cewa Najeriya ta nemi bashin dala biliyan daya domin cike gibin kasafin kudinta na bana.

Bankin wanda ya bayana haka a shafinsa na internet, ya kuma ce nan ba da jimawa ba zai aike da wata tawaga zuwa Najeriyar, domin tattaunawa da mahukuntan kasar da sauran masu ruwa da tsaki a kan bashin.

A baya-baya nan ne mujallar Finacinal Times ta wallafa wani rahoto cewa Najeriya ta nemi bashin gaggawa daga bankin duniya da kuma bankin raya kasashen Afrika da yawansu ya kai dala biliyan uku da miliyan dari biyar.

Sai dai a farkon makon da mu ke ciki ma'aikatar kudi ta Najeriyar ta musanta rahoton, inda ita ce sam ba ta nemi bashin gaggawa daga wurin bankunan ba.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ambaci ministar kudin kasar Madam Femi Adeosun, na cewa Najeriyar na da aniyar neman rancen kudi sama da naira biliyan dubu (trillion) daya domin aiwatar da ayyuka da za su bunkasa tattalin arzikin kasar, amma suna kan tattaunawa.