Za a hukunta 'yan bangar-siyasa a Nijar

Image caption A watan da muke ciki za a yi zabe a Jamhuriyar Nijar.

Hukumomin shari'a a Jamhuriyar Nijar sun ce za su hukunta duk mutumin da yake son tayar da zaune-tsaye a kan zaben kasar da za a yi a watan nan.

Hukomomin sun ce za su dauki wannan mataki ne bayan wasu rahotanni sun ce wasu 'yan siyasa na amfani da 'yan bangar-siyasa wajen tayar da rikici.

Babban alkali na kasa na babban kotun Damagaram, Alhaji Shehu Musa, ya yi kira ga 'yan siyasa da su guji tayar da hatsaniya, yana mai cewa duk wanda aka samu da laifi zai yaba wa aya-zakinta.

A cewarsa, "Abin da muke fata shi ne kada a yi zage-zage da buge-buge ko kona wurare. Duk wanda ya yi hakan ya taka doka, kuma duk wanda ya taka doka za a tura keyarsa gaban kotu domin yi masa hukunci."

Alhaji Shehu Musa ya kara da cewa za su saurari duk wanda aka musgunawa idan ya kai karar wadanda suka zi zarafinsa, yana mai cewa bai kamata 'yan siyasa su rika yin kace-nace ba.

Su ma 'yan siyasa sun yi kira ga magoya bayansu da su kauracewa tashin hankali, suna masu yin kira a gare su da su mayar da hankali wajen hankulansu 'yan kasar domin su zabi jam'iyyunsu.