'Yan Sanda sun kai samame a Lagos

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police website
Image caption Babban Sufetan 'yan sandan Nigeria Solomon Arase

Jami'an tsaro na 'yan sanda na musanman a karkashin gwamnatin jihar Lagos sun kai wani samame a 'yan rake dake a Iddo a Lagos.

Ana gudanar da harkokin saren rake a wajen, sannan kuma masu karafin karfi na gudanar da sana'oinsu.

An samu rahotanni masu karo da juna dangane da yawan adadin mutanen da suka mutu a yayin wannan samame.

Wani da ke gudanar da sana'a a wajen ya yi zargin cewa jami'an tsaron sun kashe musu mutane sama da ashirin.

Sai dai jami'an tsaron da suka kai wannan samame sun musanta kashe ko da mutum daya.

Sai dai rundunar tsaron 'yan sandan ta musamman, ta ce an gano makamai na bindigogi da harsasai a lokacin da aka kai samamen