Shell zai kori ma'aikata 10,000

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shell ya samu riba mafi kankanta a shekarar 2015 cikin shekaru 13.

Kamfanin da ke hakar man fetur, Royal Dutch Shell, ya tabbatar cewa zai kori ma'aikata 10,000 sakamakon raguwar da ribarsa ta yi mafi muni a cikin shekara goma sha uku.

Kamfanin ya samu ribar $1.8bn a rubu'in karshen shekarar 2015, idan aka kwatanta da wacce ya samu ta $4.2bn a rubu'in karshen shekarar 2014.

Kazalika, kamfanin ya samu ribar $3.8bn a shekarar 2015, sabanin wacce ya samu ta $19bn a shekarar 2014.

A makonni biyu da suka wuce new kamfani ya nuna cewa zai samu riba mafi kankanta a cinikin da yake yi.

A watan jiya, masu hannun jari a kamfanin na Shell, wanda shi ne kamfanin mai mafi girma a Turai, sun amince ya sayi kamfanin BG Group.

Da ma kamfanin ya ce zai kori ma'aikata 10,000 idan ya yi nasarar sayen kamfanin BG, a matsayin wata hanya ta yin tsimin kudi.