Ana cece-kuce kan tattaunawar sulhun Syria

Zauren tattauna a Geneva Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ba a cimma matsaya ba kan tattaunawar sulhun da aka dade ana son cimma.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya zargi gwamnatin Syria da taimakon babbar kawarta Rasha da yin kafar Ungulu ga yin amfani da hanyoyin siyasa dan magance yakin basasar da ake a kasar.

Mr Kerry ya yi wannan kalami ne a taron da Majalisar Dinkin Duniya ke ta shirya a Geneva, wanda aka dakatar da shi.

Su ma 'yan Adawa sun dora alhakin hakan kan ruwan bama-baman da Rasha ke yi a kasar.

Shugaban masu shiga tsakanin, Bassma Kodmani, ya shaidawa BBC cewa Amurka da sauran kasashen turai sai sun sake zage damtse dan ganin an cimma burin kawo karshen yakin da kasar Syria ke ciki na kusan shekaru biyar.

A nata bangaren gwamnatin Syria, ta zargi 'yan adawa da yin bita da kulli kan rashin tattaunawar.

Jakada na musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Syria, Staffan de Mistura, yace za a ci gaba da tattaunawar zuwa karshen wannan wata.