Buhari ya tura tawaga zuwa Dalori

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mata da kananan yara na cikin wadanda suka fi shan wuya a hare-ahren da Boko Haram ke kai wa.

Wata tawagar gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Tarayyar Nigeria, Mista Babacir David Lawal, ta kai wata ziyarar ta'aziyya zuwa kauyen Dalori na Jihar Borno.

A karshen makon da ya wuce ne 'yan Boko Haram suka kashe mutane fiye da hamsin a garin, tare da lalata dukiya da kuma kone gidaje.

Tawagar ta je Maiduguri ne bisa umurnin Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari.

Tawagar ta ce gwamnatin Nigeria za ta gyra garin, sanna ta ci gaba da ba su tsaro, ko da ya ke ta yi kira ga mazauna irin wadannan yankuna da su rika kai rahoton duk wani mutum da ba su yarda da shi ba, domin gujewa kaddamar da irin harin da aka kai msu.