Ayyukan Noma sun bunkasa a Nijar

Wani Manomin Rogo
Image caption Manoma a jamhuriyar Nijar sun samu sassaucin yin shuka da girbi.

Ayyukan da hukumar ta 3N ke yi dai sun taimaka wajen cimma muradin karni na fannin rage adadin masu fama da karancin abinci da kashi 50 cikin 100 a kasar, kuma hukumar samar da abinci ta duniya FAO ta tabbatar da haka.

Manoma a jamhuriyar Nijar sun shaidawa BBC a yanzu su kam Alla-san barka su ke, dan sun samu sassauci a ayyukansu musamman manoman Rani da aka ba su injinan ban ruwa, da Iri na zamani da ya ke saurin fitowa.

An kuma samar da kayan aikin gona na zamani, ba kamar da can da suke amfani da hannu wajen yin Shuka har ma da Girbi.