An rage hawa manyan motoci a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Faduwar farashin mai na tasiri a Najeriya

Faduwar farashin man fetur a duniya ta janyo raguwar sayen manyan motoci kirar Porsche da kimamin kashi hamsin cikin dari.

A baya, lokacin da ake samun kudi sosai, 'yan Najeriya masu hannu da shuni su kan sayi irin wadannan manyan motocin.

Manajan Daraktan, kamfanin sayar da Porsche a Lagos, Parvin Singh ya shaida wa BBC cewar kasuwar motar ta fadi da kashi hamsin cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar 2014.

A cewarsa, a yanzu attajirai sun kauracewa kamfanin saboda farashin mai ya fadi a duniya.

Man fetur ne ke samar da kashi saba'in cikin dari na kudaden shigar gwamnatin Najeriya, kuma idan gwamnati ta dakatar da kashe kudi, to hakan na matukar tasiri ga 'yan kasuwa masu zaman kansu a kasar.