Saudiyya za ta shiga yaki da IS a Syria

Mayakan IS Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Saudiyya a shirye ta ke dan taimakawa a kawar da kungiyar IS a Syria.

Sakataren Tsaron Amurka Ash Carter ya yi maraba da tayin da kasar Saudiyya ta yi na samar da dakarun kasa domin yaki da kungiyar IS a Syria.

Kamfanin dillacin labaru na Reuters ya ambato Mr Carter yana cewa Amurka na shirin tattauna wannan tayi tare da Ministan Tsaron Saudiyya a birnin Brussels a mako mai zuwa.

Mai magana da yawun rundunar sojojin Saudiyya ne dai ya ce a shirye kasarsa take ta samar da dakarun da zasu yaki kungiyar IS a Syria, idan har gamayyar sojojin da Amurka ke jagoranta ta yanke shawarar kai farmaki ta kasa.

Birgediya Janar Ahmed al-Asiri ya ce kasarsa ta yi imanin cewa idan har ana son a kawar da 'yan bindigar, ya zama wajibi a yi musu luguden wuta ta sama da ta kasa.

Kasar Saudi Arabiya ta kasance cikin kasashen da ke luguden wuta ta sama a kan mayakan na IS tun watan Satumbar shekarar 2014