Sojojin Nigeria za su koyo dabaru a Colombia

Hakkin mallakar hoto Reuters

Rundunar sojin kasa ta Nigeria ta ce dakarunta na yin ziyara a kasar Colombia ne domin su karo ilmi kan yaki da ta'addanci.

Babban Hafsan Sojin Kasa na Nigeria, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, shi ne dai ya jagoranci wata tawagar manyan dakarun sojojin kasa na kasar zuwa wasu manyan cibiyoyin sojin Colombia.

Ziyarar na zuwa ne daidai lokacin da sojojin kasa na Nigeriar ke cigaba da fafatawa da mayakan Boko Haram a arewa maso gabashin Nigeria.

Colombia dai ta yi fama da 'yan tawaye shekara da shekaru kuma a yanzu ne kasar ke kokarin kulla yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan tawayen na FARC.

Kakakin rundunar sojin kasa ta Nigeria, Kanar Sani Usman Kukasheka, ya shaida wa BBC cewa za a koyi darasi daga ziyarar ta fuskar dabarun yakin Colombia da dangantakar sojojinsu da farar hula, ta yadda za a tabbatar ba a musgunawa wadanda ba su ji ba ba su gani ba a lokacin yaki.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Sai dai Nigeria ba ta nemi taimakon sojojin Colombia ba dangane da yakin da take yi da Boko Haram a arewa maso gabas.