Syria za ta samu taimakon dala biliyan 10

Image caption Kasashe 70 ne suka yi alkawarin taimakawa Syria

Shugabannin kasashen duniya da ke taro a London sun alkawarta ba da kudi fiye dala bilyan goma don taimaka wa mutanen Syria da yaki ya raba da muhallinsu.

Firai ministan Biritaniya, David Cameron, ya ce wannan gidauniya ita ce aka fi tara kudi mafi yawa don wani agajin jin kai.

Ya ce za a iya amfani da kudin wajen handa 'yan gudun hijira jin cewa sai sun saka rayukansu cikin hadari wajen kama hanya zuwa Turai.

A waje daya kuma mahukunta a Turkiyya sun ce dubban 'yan gudun hijirar Syria sun nufi kan iyakar Turkiyya a yunkurin da suke yi na kaucewa yakin da ake yi a birnin Aleppo.

A 'yan kwanakin da suka wuce dai, jiragen yakin Rasha sun taimakawa sojin Syria suka kara nausawa zuwa yankin na Aleppo.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kakkausar suka a kan ci gaba da kai hari da Rasha ke yi a kasar ta Syria, yana cewa hakan ya sanya duk wani yunkurin zaman lafiya ya zama bai da wani amfani.